Gwamnatin jihar Rivers ta baiwa Dakubo Asari sarauta
ARTICLE AD BOX
Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya naɗa Dokubo Asari a matsayin Sarkin Torusarama Piri a Ƙaramar Hukumar Degema.
An gudanar da taron ne a fadar gwamnati da ke Fatakwal a yau Laraba
Gwamna Fubara, yayin da yake gabatar da sandar mulki ga Dokubo, ya yi kira gareshi da ya yi amfani da mukaminsa wajen inganta zaman lafiya, tsaro, da cigaba a yankinsa.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɓaka ci gaban al’umma.
“Madadin gwamnati, ina taya ku duka hudu murna. Zuwa wannan matsayi ba abu ne mai sauƙi ba, kuma nasan kun yi aiki tukuru don kaiwa wannan matsayi. Wannan amincewa ba don amfanin kanku aka yi ba, sai don alhakin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankunanku,” inji gwamnan.
“Ba na so ku dauki wannan matsayin a matsayin wata dama don haifar da rikici. Duk da cewa muna da ikon janye wannan amincewa, ba ni da niyyar yin hakan. Ina son ku haɗa kai da mu don tabbatar da cigaba,” ya ƙara da cewa.
Baya ga Dokubo, wasu da aka nada sun haɗa da Winston Odize Alamina Oputibeya na 12, Sarkin Koniju a Ƙaramar Hukumar Okrika; da Eze Noble Friday Uwoh (CSP mai ritaya), Eze Igbu-Ehuda (Ahoada) na 4 a Ƙaramar Hukumar Ahoada-East; da Yariman Ike Ehie, Eze Igbu Orilukwoe, shima a Ƙaramar Hukumar Ahoada-East.